in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yarjejeniyar batun nukiliyar Iran tana shafar tsaron EU
2018-05-29 11:18:36 cri
Babbar wakiliyar Tarayyar Turai (EU), mai kula da harkokin diflomasiyya da manufofin tsaro, Federica Mogherin ta bayyana a jiya Litinin cewa, batun nukiliyar kasar Iran na shafar tsaron kungiyar, maimakon tattalin arziki.

Kungiyar EU ta kira taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobinta a jiya, inda suka tattauna batutuwan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da yanayin yankin Gaza da kuma na Syria da dai sauransu. Bayan taron, Federica Mogherin ta bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, idan babu yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, yanayin tsaron yanki da kungiyar EU zai shiga cikin mawuyacin hali.

A watan Yulin shekarar 2015, kasar Iran da kasashen shida da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa, watau kasashen Amurka, Burtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, suka kulla cikakkiyar yarjejeniyar batun nukiliyar kasar Iran, inda Iran ta yi alkawari dakatar da shirinta na makaman nukiliya, tare da yin amfani da makamashin nukililya wajen biyan bukatun jama'a, sa'an nan, gamayyar kasa da kasa suka soke takunkumin da suka kakaba mata.

Amma a ranar 8 ga watan nan ne, kasar Amurka ta sanar da janye jiki daga yarjejeniyar, da kuma dawo dukkan takunkuman da ta taba sanyawa kasar Iran. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China