in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin tattaunawar kafofin yada labarai na Sin da Afirka karo na 4
2018-06-26 13:35:42 cri

A yau Talata ne aka bude taron dandalin tattaunawar kafofin yada labarai na Sin da Afirka karo na 4 a birnin Beijing. Wakilai na hukumomin gwamnatoci da kafofin yada labarai na Sin da Afirka su 460 ne suke halartar taro na wannan karo.

A yayin taron, wakilai guda 460 wadanda suka zo daga kasashe 45, sun tattauna kan batutuwan da suka shafi manufofin kafofin yada labarai na Sin da Afirka, da karfafa ikon Sin da Afirka a fannin yada labarai tsakanin kasa da kasa, da kuma raya fasahohin zamani na kafofin yada labaran Sin da Afirka da dai sauransu.

Babban makasudin gudanar da wannan taro shi ne ci gaba da aiwatar da sakamakon da aka cimma a yayin taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka na shekarar 2015, wanda aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, da kuma habaka hadin gwiwa da mu'amalar dake tsakanin kafofin yada labarai na Sin da Afirka.

Haka kuma, a yayin taron, wasu kafofin watsa labarai na Sin da Afirka sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda 12, yayin da kuma aka zartas da shirin karfafa hadin gwiwa tsakanin kafofin yada labarai na Sin da Afirka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China