Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan sandan sun yi bore ne bisa zargin rashin biyan su hakkokinsu na albashi, da alwasu-alwasu. Sai dai jim kadan da aukuwar al'amarin, rundunar 'yan sandan kasar ta fidda wata sanarwa dake karyata aukuwar boren.
Sanarwar da kakakin rundunar Jimoh Moshood ya rabawa manema labarai, ta ce 'yan sandan sun gabatar da korafin su ne kawai, kuma nan take suka koma bakin aikinsu.
Kaza lika ta bayyana cewa, rashin rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar nan ta 2018 ne ya haddasa jinkirin biyan 'yan sandan hakkokin su, kuma da zarar shugaban kasar Muhammadu Buhari ya amince da kasafin, dukkanin matsalolin da ake fuskanta za su zama tarihi.
Wasu rahotanni sun tabbatar da isar babban sifeton 'yan sandan Najeriyar Ibrahim Idris fadar shugaban kasa a jiya Litinin, inda ya yada zango a ofishin sakataren gwamnatin kasar Abba Kyari, gabanin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari. (Saminu Hassan)