in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NSCDC ta baiwa jami'ai 550 horo don yaki da 'yan ta'adda a Zamfara
2018-07-01 15:34:36 cri

Labarin da muka samu daga shafin Intanat na Leadershipayau kan cewar, hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya wato NSCDC a takaice, ta bi sahun rundunonin tsaro na kasar don kawo karshe 'yan ta'addan da suka addabi jihar Zamfara, inda hukumar ta baiwa jami'anta 550 horo.

Kwamandan hukumar, D.A. Abi ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci dakarun da suka samu horon a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Kwamanda Abi ya kuma bayyana cewa, wannan horon ya samu amincewar babban kwamandan sojojin kasa wanda ya jagoranci bada horon na tsawon watanni uku ya kara da cewa, kawo yanzu sun samu nasarar horar da jami'ai 550 yadda zasu sarrafa bindiga da kuma dabarun yaki da 'yan ta'adda. Sakamakon samun wannan horo jami'an nasu ba zasu ji shakkar shiga ko ina ba don fatattakar 'yan ta'adda da 'yan Sara-Suka da barayin shanu a fadin jihar ta Zamfara."

Kwamandan ya yi kira ga shugabannin kananan hukumomi dasu gyarawa jami'an ofisoshinsu don su samu wuraren da zasu adama makamansu domin tunkarar 'yan ta'addan. Kwamandan ya kuma yabawa shugaban rundunar sojoji Birgediya Janar L. M. mai kula da bataliya ta 223 dake Gusau, da Gwamna Abdula'aziz Yari Abubakar sakamakon daukar nauyin bada horon.

A nasa jawabin Shugaban huhumar NSCDC na kasa Abdullahi Gana Muhammad, ya bayyana gamsuwa game da horar da jami'an, kana ya bayyana cewa rundunarsa ta shirya tsaf don ganin sun fatatakin 'yan ta'addan da suka addabi jihar Zamfara da kasa baki daya, kana wannan horon zai karawa rundunar kwarin gwiwa wajen fatattakar 'yan bindigar.

A nasa bangaren Gwamna Abdula'aziz Yari na jahar Zamfara yace gwamnatin jihar na iyakar kokarinta wajen taimakon jami'an tsaro.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China