Kwamishinan Lafiya na jihar Kennedy Ishaya, ya ce tuni Gwamnati ta dauki matakan shawo kan cutar da ta barke a jihar a baya-bayan nan.
Kennedy Ishaya, wanda ya ce marasa lafiyar da dukkansu dalibai ne na wata makarantar Islamiyya a Gomben, ya ce gwamnatin na kula da su kyauta, inda ya kara da cewa, an samar musu da isassun magunguna.
Kwalara kwayar cuta ce wadda kan haifar da matsananciyar gudawa da zai iya kai wa ga mutuwa idan ruwan jikin mutum ya kare.
Barkewar cutar abu ne da aka saba gani a Nijeriya saboda rashin kyan tsarukan samar da ruwa, musamman a yankunan dake da cunkoson jama'a. (Fa'iza Mustapha)