in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon shugaban Najeriya ya bukaci shugabannin Afirka da su rika yin canje-canje a tsarin shugabancinsu
2018-06-28 09:40:27 cri
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi kira ga shugabannin kasashen Afirka da su rika aiwatar da canje-canje a tsarin tafiyar da harkokin mulki.

Obasanjo wanda ya yi kiran yayin da yake jawabi a wani taro da aka shirya a Abuja, fadar mulkin Najeriya, ya gano wasu fannoni kamar zaman lafiya da tsaro, shugabancin na gari da rage talauci a matsayin muhimman sassa guda uku da nahiyar ya kama ta gaggauta yiwa gyaran fuska domin ta bunkasa alakarta da abokan huldarta ciki har da kasar Sin.

Ya ce, idan aka kalli wadannan muhimman fannoni uku, za a ga irin nasarorin da kasar Sin ta samu a gida da kuma waje da ma alkawuran da kasar Sin ta daukawa kanta, da makwabtanta har ma da abokan huldarta, musamman a kasashen Afirka. Da ya juya ga bangaren kawar da talauci kuwa, tsohon shugaban Najeriyar, kana tsohon shugaban kungiyar tarayyar Afirka, ya ce kasar Sin kyakkyawar abin misali ce a fannin kawar da talauci. Inda ya yi nuni cewa, illar talauci tana tasiri a Afirka, don haka wajibi ne a samo hanyar kawar da wannan matsala.

Ya ce, kamata ya yi batun kawar da matsalar talauci ya kasance abin da nahiyar za ta mayar da hankali a kai a sabon alakarta da kasar Sin. A don haka ya bukaci shugabannin nahiyar da su zage dantse wajen ganin sun gudanar da shugabanci na gari.

Manufar taron na Abuja wanda ya samu halartar wasu shugabannin nahiyar da suka hada da tsohon shugaban Jamhuriyar Congo Boni Yayi, da tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamane Ousmane, ita ce tattauna sabon yanayin alakar Sin da Afirka. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China