in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zargi wani gungun makiyaya da kaddamar da kisan al'umma a Plateau
2018-06-26 19:41:59 cri
Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ko MACBAN a takaice reshen yankin tsakiyar Najeriya Danladi Ciroma, ya ce wasu rukunin makiyaya ne suka kaddamar da harin baya bayan nan a jihar Plateau, a wani mataki na ramuwar gayya.

Danladi Ciroma, wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce harin wanda ya sabbaba kisan mutane sama da 80, ramuwa ce kan wasu hare hare da aka kaiwa Fulanin makiyaya, tare da sace masu shanu.

Ya ce an samu tashe tashen hankula tsakanin manoma 'yan kabilar Berom da Fulani makiyaya. Kuma tabbas an san wadanda suke tada hankula tsakanin al'ummun yankin, sai dai kawai wasu daga 'yan uwan su na ba su kariya. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China