in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane da dama ne ake fargabar sun mutu yayin wata motar dakon mai ta yi bindiga a Najeriya
2018-06-29 10:33:09 cri
Rahotani daga tarayyar Najeriya na cewa, mutane da dama ne ake fargabar sun mutu, yayin da wata babbar motar dakon mai ta yi bindiga a yammacin jiya Alhamis a cunkoson ababan hawa a birnin Legas, cibiyar kasuwancin kasar.

Shaidun gani ido na cewa, hadarin ya faru ne a kan wata gada, lokacin da motar ke kokarin fita daga Legas zuwa tagwayen hanyar Legas zuwa garin Badun dake yankin kudu maso yammacin kasar.

Budu da kari, hayakin da ya turnuke sanadiyar gobarar da ta tashi, ya lullube motoci da dama, lamarin da ya kai ga dakatar da kai komon motoci a dukkan sassan hanyar, yayin da jami'in agaji ke kokarin kashe wutar da ma taimakawa wadanda hadarin ya rutsa da su.

Wani direban motar bas din haya mai suna Gbolahan Adebisi, da lamarin ya faru a kan idonsa, ya ce an dan samu tsaikon zirga-zirgar ababan hawa a lokacin da motar ta yi bindiga. Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, jami'in agaji na cewa, kimanin motoci 60 ne hadarin ya shafa,ana kuma ci gaba da aikin ceto.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China