A jawabinsa, jakadan Sin dake kasar Burundi Li Changlin ya bayyana cewa, shekarar 2018 shekara ce ta cika shekaru 55 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Burundi, kana a shekarar za a shirya taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka a birnin Beijing, kuma kasar Burundi za ta halarci taron, wannan zai taimaka wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
Shi ma a nasa jawabin ministan harkokin wajen kasar Burundi Alain Aime Nyamitwe ya bayyana cewa, a shekarun baya baya nan dangantakar dake tsakanin Burundi da Sin na bunkasa yadda ya kamata. Ya ce gwamnatin kasar Sin ta taimakawa kasar Burundi wajen gina fadar shugaban kasar, da samar da hatsi cikin gaggawa da sauransu, wadanda suka taimakawa kasar Burundi sosai. (Zainab)