Oshiomole mai shekaru 66, ya kama rantsuwar aiki ne jiya Lahadi a Abuja, babban birnin kasar, bayan kammala babban taron jam'iyyar na yini biyu.
Babban taron jam'iyyar da aka fara ranar Asabar da ta gabata ya samu halartar shugaban kasar Muhammadu Buhari da manyan jami'an jam'iyyar na kasa da na jihohi.
Oshiomole wanda makusancin Buhari ne a harkar siyasa, ya tsaya neman shugabancin Jam'iyyar ne ba tare da abokin hammaya ba.
Magabacinsa John Odigie Oyegun, wanda shi ma dan jihar Edon ne ya sha suka daga wasu 'yayan jam'iyyar gabanin babban taron. (Fa'iza Mustapha)