in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A mai da aikin siyasa na JKS a matsayin aikin tushe na jam'iyyar, in ji Xi Jinping
2018-06-30 16:15:55 cri
Hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya ta Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, ta kira taron karawa juna sani karo na 6 jiya da yamma, domin karfafa aikin siyasa na Jam'iyyar. A yayin taron, babban sakataren kwamitin tsakiyar, kuma shuagaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, aikin siyasa na jam'iyyar shi ne aikin din din din da za a yi nazari a kai. Ya ce ya kamata Jam'iyyar Kwaminis ta Sin ta ci gaba da jagorantar aikin siyasa, domin karfafa karfinta na gudanar da wannan aiki.

Cikin jawabinsa, Xi Jinping ya bayyana cewa, aikin siyasa shi ne aikin dake kan gaba wajen neman ci gaban jam'iyyar, wanda ke da muhimmiyar alaka da makomarta. Kana, hanyar siyasa da za a bi ita ce babban burin tsarin gurguzu na kasar Sin. Sa'an nan kuma, burin " cika Shekaru 100, Guda Biyu" shi ne babbar manufar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, wato na gina zaman takewar al'umma mai walwala bisa dukkan fannoni zuwa lokacin cika shekaru dari da kafuwar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, a shekarar 2021, da kuma gina kasa mai tsarin gurguzu, wadda ta samu wadata da dimokuradiyya da wayewar kai da kuma daidaito a lokacin cika shekaru dari da kafuwar sabuwar kasar Sin, a shekarar 2049.

Haka kuma, Xi Jinping ya ce, tushen tsarin gurguzu na kasar Sin, ya na karkashin jagorancin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar, kuma ya kamata a mai da hankali kan bukatun al'ummar kasa domin karfafa aikin siyasa na jam'iyyar, da mayar da aikin tallafawa al'umma, da kuma neman goyon bayan al'umma a matsayin aiki mafi muhimmanci. Inda ya ce kamata ya yi su rika gudanar da ayyukansu tare da al'ummar kasa da daukar bukatun al'umma matsayin bukatunsu na kansu, domin la'akari da al'ummar kasa ko da yaushe. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China