in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayar da rahoton cikakken zaman taro na 3 na kwamitin tsakiyar JKS karo na 19
2018-02-28 20:12:17 cri

A ranar 26 zuwa 28 ga wata ne aka shirya cikakken zaman taro na 3 na kwamitin tsakiyar JKS karo na 19 a nan birnin Beijing, inda babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping ya yi jawabi.

A yayin taron, an saurari tare da tattauna rahoton ayyuka da shugaba Xi ya gabatar a madadin ofishin siyasar kwamitin koli na JKS kana aka duba tare da zartas da takardar sunayen jami'an hukumomi da za a gabatar wa zaman taron na 1 na majalisar wakilan jama'a karo na 13, da takardar sunayen jami'an majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar da za a gabatar wa zaman taro na 1 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa karo na 13, kana an tsaida kudurin gabatar da wadannan takardun biyu ga kwamitocin zartarwa na tarrukan biyu.

Baya ga haka, an yi nazari tare da zartas da kudurin kwamitin koli na JKS game da zurfafa yin kwaskwarima kan hukumomin jam'iyya da na kasa, da shirin zurfafa yin kwaskwarima kan hukumomin jam'iyya da na kasa, kana an amince a gabatar wa zaman taron na 1 na majalisar wakilan jama'a karo na 13 wasu abubuwa da aka shirin don a yi nazari a kansu kamar yadda doka ta tanada.(Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China