in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da taron tattaunawa a tsakanin manyan jami'an JKS da jam'iyyun kasashen duniya
2018-05-21 13:29:43 cri
Za a gudanar da taron tattaunawa a tsakanin manyan jami'an jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyun sauran kasashen duniya, wanda hukumar cudanya da kasashen waje ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin za ta karbi bakunci tsakanin ranekun 26 zuwa 28 ga wannan wata a birnin Shenzhen na kasar Sin, inda za a gudanar da taro mai taken "labarin jam'iyyar kwaminis ta Sin a lardin Guangdong a karkashin bin tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki", da taron tattaunawa game da cika shekaru 200 da haihuwar Karl Marx, da dandalin taron shugabanni matasa na kasar Sin da na kasashen Afirka karo na 4, da kuma dandalin tattaunawa a tsakanin jam'iyyun Sin da kasashen Latin Amurka karo na 2.

A wannan lokaci ma, hukumar cudanya da kasashen waje ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, za ta gudanar da dandalin tattaunawa a tsakanin jam'iyyun kasashe membobin kungiyar SCO karo na farko a birnin Shenzhen. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China