in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CCDI ta kara yin bayani game da tsarinta na sanya ido
2018-02-13 11:13:42 cri
Hukumar sanya ido da ladaftarwa ta JKS (CCDI) ta bayyana cewa, a shekarar 2018 da muke ciki, za ta kara mayar da hankali wajen sanya ido kan matakan zurfafa gyare-gyare na kasar.

Wani rahoton aiki da sakataren hukumar ta CCDI Zhao Leji ya gabatar yayin cikakken zama na biyu karo na 19 na hukumar, ya ce kamata ya yi hukumar ta kara yin hadin gwiwa da majalisar wakilan jama'a ta NPC, ta kuma ba da damar amincewa da wasu dokokin sanya ido, da kafa hukumar sanya ido yayin zaman majalisar na NPC na 13 da za a bude a ranar 5 ga watan Maris na wannan shekara.

A cewar rahoton, manufar zurfafa yin gyare-gyare game da tsarin sanya ido, shi ne kara karfin shugabancin JKS a aikin da take na yaki da cin hanci, ta yadda za ta zamantar da tsarin kasar da karfin ta na tafiyar da harkokin mulki.

Mr Zhao ya kuma yi kira ga jagororin yaki da cin hanci a kasar da su nazarci su kuma aiwatar da tunanin Xi Jinping game da tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki, gami da sakamakon babban taron wakilan JKS karo 19.

Ya kuma bukaci hukumar ta CCDI da ta kare matsayin shugaba Xi a matsayin jagoran kwamitin koli na JKS da kuma jam'iyyar baki daya, da ikon kwamitin koli na JKS da jogarancinta na bai daya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China