Littafin mai babi 16 ya kushi tarihin nasarori da canje-canje da kasar Sin ta samu, tun lokacin da aka fara aiwatar da manufar bude kofa da yin gyare-gyare da zamanantar da tsarin gurguzu a taron wakilan JKS karo na 18, da muhimman tunani da ra'ayoyi, da hukunce-hukunce da matakan da aka dauka a taron wakilan JKS karo na 19.
Bugu da kari, sassan rahoton zai taimakawa masu karatu kara fahimtar ruhin taron wakilan JKS karo na 19 da baiwa kasashen duniya damar fahimtar yadda JKS ke amfani da dabaru da tsarin tafiyar da harkokin jam'iyyar, da matakan raya kasa da kasar Sin za ta dauka da kuma manufofin diflomasiya da na cikin gidan kasar Sin.
Za kuma a wallafa littafin cikin harsunan Faransanci, Rashanci da Larabci da Sifaniyanci da Portuguese da Jamusanci da kuma Japananci.
A ranar 18 ga watan Oktoban shekarar 2017 da ta gabata ce ne shugaba Xi ya gabatar da wannan rahoton mai taken " Matakan samun nasarar gina al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni da kokarin samun nasarar gina tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki".(Ibrahim)