in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF: Yara 210 kungiyoyi masu dauke da makamai suka sako a Sudan ta kudu
2018-05-19 15:50:03 cri
Asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF ya sanar a jiya Juma'a cewa, kimanin yara 210 ne kungiyoyin masu dauke da makamai a Sudan ta kudu suka sako a yayin wani biki da suka shirya, wanda shi ne irinsa na uku da suka gudanar a wannan shekara.

UNICEF ta bayyana cewa, kawo yanzu adadin yaran da kungiyoyin suka saki a wannan shekarar ta 2018 ya tasamma 806, kuma ana sa ran kara sako wasu yara a watanni masu zuwa, wanda idan aka hada baki daya adadin zai kai yara 1000 da za'a sako a kasar gaba daya.

A lokacin bikin na ranar Alhamis, an raba yaran da makamai, kuma an ba su kayayyakin sawa na fararen hula, UNICEF ta kara da cewa, za'a bincika lafiyar yaran daga bisani kuma a yi kokarin sauya musu tunani.

Da zarar yaran sun hadu da iyalansu, za'a samar musu da tallafin abinci na tsawon watanni uku domin taimaka musu wajen dawowa cikin hayyacinsu, kana za'a kuma ba su horo na sana'o'in dogaro da kansu da nufin inganta hanyoyin samun kudaden shigar iyalansu da kuma samun abinci. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China