in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaba na farko na Sudan ta kudu ya sanar da tarwatsa jam'iyyar adawa dake karkashin jagorancinsa
2018-05-08 14:10:11 cri

Mataimakin shugaba na farko na Sudan ta kudu Taban Deng Gai, ya sanar da tarwatsa jam'iyyar adawa(SPLM-IO) dake karkashin jagorancinsa, a jiya Litinin 7 ga wata don kawo karshen rikicin soja a kasar.

A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana a birnin Juba, hedkwatar kasar, Deng Gai ya bayyana cewa, an kawo karshen jam'iyyar da ya jagoranta, an kuma shigar da ita cikin jam'iyyar SPLM mai mulki, karkashin jagorancin shugaban kasar Salva Kiir Mayardit. Kaza lika sojojin jam'iyyar SPLM-IO, sun shiga rundunar gwamnati wato rundunar 'yantar da jama'ar Sudan.

A nasa bangaren, Mista Deng Gai ya ce, yana fatan kawo karshen rikicin soja da kasar ke fuskanta a shekarun baya-baya nan ta wannan hanya, don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar a nan gaba. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China