Huang Kunming, ya bayyana hakan ne yayin taron wakilai mahalarta taro karo na 4, na dandalin kafofin watsa labaran Sin da nahiyar Afirka wanda ya gudana a nan birnin Beijing.
Ya ce manufar Sin game da nahiyar Afirka na kunshe da aminci, da samar da nasarori na zahiri, da gaskiya tare da imani da juna, wanda hakan ke bunkasa alakar sassan biyu. (Saminu Hassan)