in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An Damke 'Yan Nijeriya 32 a Amurka
2018-06-15 12:36:15 cri

Wasu rahotanni da shafin Intanet na "Leadership A Yau", dake Najeriya ya wallafa a jiya, sun nuna cewa, hukumar bincike ta kasar Amurka ta kama wasu mutane 74 dake damfarar jama'a kudade ta yanar gizo, kuma 32 daga cikinsu 'yan Nijeriya ne

Wasu daga cikin wadanda aka kama din suna aiki ne tare da manyan kungiyoyin 'yan damfara na duniya, wasun su kuma suna damfarar ce su kadai.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa, an yi nasarar kamen ne biyo bayan wani matakai na musamman da hukumar bincken manyan laifuffuka ta Amurka FBI da sauran hukumomi dake dakile hanyoyin da 'yan damfara kan yi amfani da su wajen aiwatar da muguwar sana'arsu a duniya suka aiwatar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China