in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta yi koyi da kasar Sin wajen bunkasa fannin kimiyya da fasaha
2018-06-20 09:50:11 cri
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana kokarin koyi da kasar Sin domin bunkasa fannin kimiyya da fasaha da kirkire kirkire.

Da yake jawabi a lokacin bikin bada lambar yabo ga wasu ma'aikatan gwamnati da suka ji fice a Abuja, ministan kimiyya da fasaha na kasar Ogbonnaya Onu ya ce gwamnatin Najeriya ta lura da irin muhimmancin da fannin na kimiyya da fasaha ke da shi wajen bunkasa tattalin arzikinta.

Onu ya ce Najeriya za ta yi koyi daga kasar Sin kasancewar kasar tana da burin zama jagora a fannin kimiyya da fasaha a nahiyar Afrika.

Ministan ya fadawa mahalarta taron cewa kasar Sin ta cimma nasarori masu yawa a dukkan fannonin kimiyya da fasaha.

Onu ya ce gwamnati ta kara mayar da hankali wajen kara yawan bincike a fannin kirkire kirkire da kuma kara wayar da kan 'yan Najeriya game da muhimmancin fannonin kimiyya da fasaha da kuma kirkire kirkire.

A watan Augastan bara, majalisar zartaswa ta Najeriyar ta amince da wani sabon shiri na shekaru 13 na yin garambawaul a fannin kimiyya da fasaha, inda aka tsara shirin zuwa na gajeren zango, matsakaici da kuma na dogon zango don aiwatar da shirin ci gaban kimiyya da fasaha, da kuma kirkire kirkire a matsayin shirin da zai bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China