Yayin ziyarar ta Shugaba Buhari, kasashen biyu, sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa 3, da suka hada da aikin shimfida babban bututun iskar gas da ya ratsa yankunan kasashen 2, da samar da masana'anta a Nijeriya wadda za ta rika samar da sinadarin ammonia da sauran kayayyaki dangoginsa da kuma kafa wani tsari kan koyar da sana'o'in noma da sa ido.
Shugaban na Nijeriya, ya gana da Sarkin Morocco da Firaminista da shugabannin majalisun dokokin kasar 2.
Ya kuma kai ziyara kwalejin horar da limamai da malaman addini ta Sarki Mohammed na VI, kwalejin dake koyar da matsakaitan akidun addinin musulunci, da 'yan Nijeriya da dama ke karatu a nan. (Fa'iza Mustapha)