in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin ruwa: Sama da bakin haure 600 aka ceto a tekun Libya
2018-06-26 11:13:27 cri

Rudunar tsaron tekun kasar Libya ta sanar a jiya Litinin cewa, sama da bakin haure 600 ta ceto a sintiri daban daban da ta gudanar a tekun yammacin kasar.

Kasar Libya ta kasance tamkar wata matattara da bakin haure ta barauniyar hanya ke amfani da ita a kokarinsu na tsallakawa zuwa kasashen Turai ta Bahar Rum, hakan yana faruwa ne sakamakon tabarbarewar al'amuran tsaro da tashin hankali da ya daidaita kasar.

Sakamakon samun kawun yanayi ya sa ana samun karuwar bakin haure dake kokarin tsallakawa Turai daga kasashen Afrika da yankin gabas ta tsakiya, musamman ta tekun kudancin kasar Libya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China