in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sako ma'aikata 'yan Turkiyya da aka yi garkuwa da su a kudancin Libya
2018-06-24 15:54:09 cri
Gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDD ta sanar a jiya Asabar cewa, an sako ma'aikatan nan 3 'yan kasar Turkiyya wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a kudancin Libya a shekarar da ta gabata.

An sako kwararrun ma'aikatan 3 na kamfanin ENKA Teknik na kasar Turkiyya ne da yammacin jiya Asabar, wadanda ke aiki a cibiyar samar da iskar gas na (Obari gas power plant), tare da taimakon jami'an tsaro, kamar yadda sashen yada labarai na ofishin firaiministan kasar Fayez Sarraj ya sanar.

Sanarwar ta ce, tuni ma'aikatan uku suka bar yankin na Obari zuwa birnin Tripoli, inda daga can kuma za su koma kasarsu ta ainihi.

Sanarwar ta ce, firaiministan kasar ya yi matukar nuna damuwarsa game da halin da mutanen suka shiga, kana ya kuma nuna damuwa bisa tsaikon da aka samu na aikin samar da tashar iskar gas din ta Obari, wanda ake sa ran za ta bayar da gagarumar gudunmowa wajen warware matsalolin lartarki a kasar ta Libya.

A ranar 3 ga watan Nuwamba ne wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wane ne ba suka yi garkuwa da ma'aikata baki 'yan kasashen waje su 4, uku daga cikinsun 'yan kasar Turkiyya ne, guda kuma dan kasar Jamus, wadanda ke aiki a tashar samar da iskar gas ta Obari, mai tazarar kilomita 1,100 daga Tripoli babban birnin kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China