in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Libya ta jaddada bukatar amincewa da dokokin zabe
2018-06-21 09:03:54 cri
Kakakin majalisar dokokin kasar Libya wanda ke da ofishinta a gabashin kasar Agila Saleh ya jaddada aniyar amincewa da dokokin zaben shugaban kasar da na majalisar dokokin kasar Libyan dake tafe.

Saleh ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake ganawa da mataimakinsa, Fah'ti Al-Maremi, kamar yadda mashawarci ga Agila Saleh a banagaren yada labarai ya tabbatar da hakan.

A kwanan baya ne kasar Faransa ta dauki nauyin shirya taron tattaunawa game da batun Libyan a birnin Paris wanda ya tattaro dukkan bangarorin Libya da abin ya shafa domin nazarin matakan da za'a dauka wajen kawo karshen rikicin siyasar kasar, daga bisani bangarorin sun cimma matsaya inda suka amince da a gudanar da sahihin zabe mai tsabta na shugaban kasar da majalisar dokoki a ranar 10 ga watan Disamba.

Kakakin majalisar dokokin ya nanata muhimmancin amincewa da dokokin zabe wadanda za su daidaita ranakun gudanar da zabukan kasar, sanarwar ta kara da cewa, dakarun sojojin kasar suna yunkurin kaddamar da hare hare kan 'yan bindiga wadanda suka mamaye tashoshin ruwa na albarkatun man kasar guda biyu tun a ranar Alhamsi.

Sanarwar ta ce, taron tattaunawar ya tabo muhimmancin tallafawa dakarun sojin kasar a yakin da suke yi da mayakan 'yan ta'adda wadanda ke neman kwace ikon tafiyar da harkokin jama'ar kasar Libyan, a yankunan tashar ruwa mai arzikin mai da kuma yankunan kan tudu na kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China