in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin ruwan Libya sun ceton 'yan cin rani 301 a yankin tekun kasar
2018-06-22 10:26:22 cri
Sojin ruwan Libya,sun ceton 'yan cin rani 301 a yankin tekun dake yammacin kasar a jiya Alhamis.

Kakakin sojin Ayoub Qassem, ya shedawa manema labarai a wannan rana cewa, jiragen ruwa guda biyu dake dauke da 'yan cin rani ba bisa doka ba daga kasashen Afrika da dama sun lalace, inda suka tsaya a sararin tekun dake yammacin kasar. Sojoji masu gadin gabar tekun ne suka ceto wadannan mutane 301.

Qassem ya ce, an kai 'yan cin ranin wani sansanin sojin ruwa dake birnin Tripoli hedkwatar kasar, inda daga baya za a kai su ofishin yakar shigar 'yan cin rani ba bisa doka ba na kasar. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China