Flippo Grandi, ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da aka yi jiya a Tripoli babban birnin Libya, bayan ya ziyarci sansanonin da cibiyoyin ajiye 'yan ci rani.
Ya ce akwai bukatar gaggauta shirin sake tsugunarwar, yana mai cewa wani bangare na shirin ne kadai aka aiwatar, inda aka karbi kasa da 'yan ci rani 2,000.
Ya ce an tsugunar da wani adadi kalilan a Italiya da Romania. Kuma an kai kimanin 'yan ci rani 1,300 wanda shi ne adadi mafi yawa, zuwa Niger. Yana mai godewa Gwamnatin Niger bisa shirya wani wuri na wucin gadi na karbar 'yan ci ranin.
Jami'in ya kuma yi kira da a gaggauta mayar da 'yan gudun hijirar Libya zuwa biranensu, inda ya ce 'yan gudun hijirar na ci gaba da galabaita saboda rashin wata yarjejeniya a hukumance. (Fa'iza Mustapha)