Ayob Qassem, kakakin sojojin ruwan kasar Libya, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, dakarun tsaron tekun kasar sun ceto bakin haure kimanin 82 wadanda suka fito daga kasashen Afrika daban daban a wani samame da suka kaddamar na tsawon kilomita 48 a garin Garrabulli, mai nisan kilomita 55 daga Tripoli, babban birnin kasar.
Bakin hauren dai suna cikin wani karamin jirgin ruwa na roba ne. Sun shafe sa'o'i masu yawa suna jira a cikin tekun, kafin daga bisani dakarun tsaron tekun suka iso wajen inda kuma suka ceto su a karo biyu, in ji Qassem.
Kakakin sojojin ruwan ya tabbatar da cewa, an gano gawar mutumin da ya fada tekun bayan da jirgin ruwan ya tarwatse.
A kwanaki biyun da suka gabata ma, dakarun tsaron tekun Libyan sun ceto bakin haure kimanin 191 a lokuta daban daban, kana sun tsamo gawawakin mutane 11 wadanda suka nitse a tekun. (Ahmad Fagam)