Staffan de Mistura, ya shaidawa kwamitin sulhu na MDD a jiya cewa, samar da mafita na da muhimmanci ga Syria da masu ruwa da tsaki a yankin, dama duniya baki daya. Ya na mai fatan masu ruwa da tsakin, za su sake samar da dabarun warware matsalar ta kowacce fuska.
Ya yi gargadin cewa, rahoton baya-bayan nan na yaki a Syria, tsakanin Iran da Isra'ila, alamu ne dake nuna yadda al'amura suka yi kamarin da ba a taba gani ba a yankin, tun shekarar 1973.
Jami'in ya ce, duk da cewa ba za a iya bada tabbaci game da musayar hare-haren ba, rashin samun tabbacin ma na nuna yadda yanayin kasar ya ta'azzara, da kuma yadda kasashen duniya ke kara yin fito na fito kan Syria, abun da ba a taba gani ba tun 1973. (Fa'iza Mustapha)