Ya shedawa 'yan jaridu cewa, ya gayyaci jami'ai daga kasashen Rasha, Turkiyya da Iran, domin tattaunawa a Geneva wadda zasu gudanar a farkon mako mai zuwa bayan jerin tattaunawar da ya gudanar da wasu jami'ai dake da ruwa da tsaki, ciki harda babban sakataren MDD.
De Mistura ya bayyana cewa, kasashen Rasha, Turkiyya da Iran sune suka dauki nauyin taron ganawar Sochi wanda aka gudanar a watan Mayu, wanda a lokacin ne aka samar da bayanan karshe dangane da kafa hukumar tsara kundin tsarin mulkin .
Jami'in MDDr yace yana kuma fatar ganawa da jami'an kasashen Amurka, Saudiyya, Birtaniya, Faransa, Jamus da kuma Jordan a ranar 25 ga watan Yuni.
Yace, a kokarin da suke na shirye shiryen tabbatar da kafa kwamitin kundin tsarin mulkin mallakar Syria wanda kuma kasar Syriar zata jagoranta da kanta, yace suna fatan wannan zai kasance a matsayin wani ginshikin da zai tabbatar da warware rikicin siyasar kasar.