in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Syria sun kwace tungar IS dake arewacin Damascus
2018-05-21 20:18:39 cri
Rahotanni daga Syria na cewa, sojojin kasar sun yi nasara kwace iko da yankin Hajar al-Aswad, wani muhimmin tungar mayakan IS kudu da Damascus, babban birnin kasar.

Kafar talabijin ta kasar ta ce, kwace yankin ya biyo bayan wata guda da sojojin suka kwashe suna bata kashi da mayakan, inda suka yi nasarar sake kwato wani yanki dake karkashin ikon mayakan na IS.

Tun da sanyin safiyar yau, gidan talabijin na kasar, ya ce an dakatar da tsagaita bude wuta da tsakar ranar jiya zuwa yau Litinin, domin a kwashe masu bukatar agaji daga yankin na Hajar al-Aswad kafin sojojin su ci gaba da daukar matakai a yankin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China