Guterres ya yi kira da a gudanar da bincike kan harin, musamman ga batun sake kai harin yayin da masu aikin ceto suke gudanar da aikinsu a wurin.
Guterres ya bayyana cewa, jihar Idlib "yankin rage rikice-rikice" ne da aka kafa bisa yarjejeniyar da bangarori daban daban suka cimma, kana ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su cika alkawuransu. Ya jaddada cewa, mutane kimanin miliyan 2 da dubu 300 a jihar Idlib suna fuskantar hadari, ciki har da kashi 60 bisa 100 daga cikinsu sun je wajen ne daga sauran yankunan kasar a sakamakon rikice-rikice. Guterres ya yi kira ga bangarorin da rikicin ya shafa da su daina nuna kiyayya, da kalubalantar bangarori da abin ya shafa da su tabbatar da tsaron fararen hula da ayyukan more rayuwa masu amfanin jama'a bisa dokokin jin kai na kasa da kasa. (Zainab Zhang)