in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da taron hadin gwiwa kan kayayyakin more rayuwa tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika a Kenya
2018-06-26 10:46:48 cri

Kasar Kenya ta karbi bakuncin taron hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da nahiyar Afrika, kan kayayyakin more rayuwa a jiya Litinin, yayin da ake tsaka da kiraye-kirayen bunkasa hulda da Beijing domin inganta zamanintar da tituna da tasoshin ruwa da layukan dogo da hanyoyin sadarwa a Afrika.

Ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya da Ma'aikatar sufuri ta Kenya da Kungiyar nazarin tattalin arzikin Afirka (AERC) dake da mazauni a Nairobi ne suka shirya taron na yini 2.

Babban Daraktan kungiyar AERC Lemma Senbet, ya ce kasar Sin ta zama wata abokiyar hulda wadda Afrika za ta iya dogaro da ita a fannin zamanintar da ababen more rayuwa.

Ya ce babu tantama jigon hadin gwiwar kasar Sin da Afrika shi ne sufuri da raya ababen more rayuwa.

Ya kara da cewa, kayayyakin more rayuwa da kasar Sin ta aiwatar sun inganta hadin kan yankin da bada damar shiga kasuwanni tare da raya fannin hada-hadar kudi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China