Wannan hukunci na zuwa ne bayan da wasu 'yan kasar ta Zimbabwe dake zaune a kasashen waje wadanda kungiyar lauyoyi masu fafutukar kare hakkin dan adam 'yan asalin kasar ta Zimbabwe (ZLHR) ke wakilta, suka gabatar da bukatar a gaban kotu, inda suka yi ikirarin cewa, sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka zartar a shekarar 2013 ya basu damar jefa kuri'a a lokacin da suke kasar waje.
To sai dai mataimakiyar babban mai shara'a ta kasar, Elizabeth Gwaunza, ta fada a lokacin zaman kotun cewa, babu wani muhimmanci dake tattare da wannan bukata.
Belinda Chinowawa na kungiyar lauyoyin ta ZHLR, yace wannan hukunci mummunan abin takaici ne.
A halin yanzu tsarin da Zimbabwe ke amfami da shi wajen zabe shi ne, duk wanda yake son jefa kuri'ar wajibi ne ya kasance yana zaune a cikin kasarsa, kuma zai kada kuri'ar ne a rumfunan zaben da aka tanada a kusa da inda yake zaune a duk fadin kasar. Kana an baiwa jami'an dake yiwa gwamnatin kasar aiki a wasu kasashen damar kada kuri'ar a yayin da suke ketare. (Ahmad)