in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar SADC ta ce a shirye Zimbabwe take ta gudanar da sahihin zabe
2018-04-22 15:14:50 cri
Kungiyar raya yankin kudancin Afrika SADC, ta ce a shirye Zimbabwe take ta gudanar da sahihin zabe saboda kyan yanayin siyasa da dokoki da kasar ke ciki.

Jaridar Herald ta gwamnatin kasar, ta ce Zimbabwe ta shirya gudanar da zaben ne a watan Yulin mai zuwa, wanda Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya ce za a yi bisa tabbatar da adalci.

Jaridar ta ruwaito sakataren zartaswar kungiyar SADC Stergomena Lawrence Tax na cewa, akwai kyakkyawan yanayin siyasa da na dokoki a kasar, wanda ke nuna shiryawar kasar ta gudanar da zabe da kuma sauye-sauyen da ake aiwatarwa yanzu haka.

Gwamnatin Zimbabwe ta hannun majalisar dokokin kasar na kokarin yiwa dokar zaben kasar garambawul a wani bangaren na sake fasalin yanayin zabe a kasar.

Stargomena Tax ya bukaci a gudanar da zaben kasar cikin kwanciyar hankali da lumana.

Kawo yanzu dai shugaban kasar bai ayyana ranar zaben ba, haka zalika manyan jam'iyyun kasar ba su gabatar da manufofinsu ba, inda a yanzu suke aikin zaben wadanda za su tsayar takara. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China