Wannan ne dai karo na farko da kasar Zimbabwe za ta gudanar da babban zabe, ba tare da tsohon shugaban ta Robert Mugabe ba, wanda shi ne shugaba mafi dadewa da ya taba mulkar kasar. Kana shi ma tsohon mai hamayya da shi Morgan Tsvangirai ya rasu kafin wannan zabe na bana.
Tun kama aikin sa a watan Nuwambar shekarar da ta gabata, bayan murabus din shugaba Mugabe, Mr. Mnangagwa ya rika nanata bukatar daukacin jam'iyyun kasar su kasance masu bin doka da oda, tare da kauracewa tada husuma yayin zaben dake tafe. (Saminu)