in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar kwalara ta yi sanadin mutuwar mutane 9 a Nijeriya
2018-03-24 13:01:32 cri
Ma'aikatar lafiya ta jihar Bauchi dake arewa maso gabashin Nijeriya, ta tabbatar da samun mutuwar mutane 9, biyo bayan barkewar cutar amai da gudawa a jihar.

Kawo yanzu, Jimilar mutane 324 ne aka tabbatar da cewa sun kamu da cutar a larduna 5 na jihar.

Kwamishinan lafiya ta jihar Zuwaira Hassan, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kafa cibiyar kebe mutanen da suka kamu da cutar domin ba su kulawa, inda ta ce tuni cibiyar ta fara aiki, har ma ta kwantar da mutane akalla 26.

Ta ce kazanta da bahaya a budaddun wurare, sune abubuwa da ake ganin sun haifar da barkewar cutar a jihar.

Cutar ta kwalara kan haddasa gudawa mai tsanani wadda ke kai wa ga karewar ruwa a jiki, sannan ya kan kai ga asarar rai idan aka gaza zuwa asbiti. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China