in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara yunkurin rigakafin kwalera mafi girma don taimkawa mutane miliyan 2 a Afrika
2018-05-08 13:03:36 cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta kaddamar da wani yunkurin rigakafin cutar kwalera mafi girma a duniya a jiya Litinin, wanda zai taimakawa mutane miliyan 2 a kasashen Afirka biyar, ta hanyar samar musu maganin sha na rigakafin cutar.

Hukumar ta WHO ta ce, wannan shi ne yunkurin rigakafin cutar mafi girma da aka taba samu a duniya, wanda zai yi amfani da magungunan rigakafi miliyan 15 cikin watanni 4 na farkon shekarar 2018. Idan aka kwatanta da shekaru 15 da suka gabata tsakanin 1997 da 2012, magungunan rigakafi miliyan 1.5 kadai aka yi amfani da su a fadin duniya. Alkaluman da hukumar ta samar, sun yi nuni da cewa, har yanzu cutar ta kwalera na addabar kasashen Afirka da dama.

A cewar babban darektan hukumar WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, duk da maganin sha na rigakafi da ake samarwa ka iya zama babban makami na tinkarar cutar, sauran ayyuka ma suna da muhimmanci, ciki har da samar da ruwa da muhalli masu tsabta, da cibiyoyin jiyya da ilmantar da al'umma a kan cutar da kuma horar da al'ummomi kan matakan kariya. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China