in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Ogun a Najeriya ta dauki matakan dakile yaduwar cutar kwalara
2017-06-15 09:33:33 cri

A Najeriya, jihar Ogun dake kudu maso yammacin kasar ta tsaurara matakan sa'ido don dakile yaduwar annobar cutar kwalara a duk fadin jihar.

Babatunde Ipaye shi ne kwamishinan lafiya na jihar, ya bayyana wa taron jama'a a yankin Sagamu dake jihar cewa, matakan da ake dauka za su yi matukar taimakawa wajen ba da riga-kafin barkewar cutar a jihar.

Ya ce, jihar Ogun ta shafe shekaru masu yawa ba ta fuskanci annobar kwalara ba, sakamakon matakan da take dauka na yin riga-kafi a matsayin babbar hanyar kariya daga kamuwa da cutar.

Ya kara da cewa, jihar tana amfani da tsarin sa'ido ne don kaucewa barkewar cutuka, inda haka ya baiwa jihar lambar yabo ta jihar da ta fi daukar matakan sa'ido don kandagarkin kamuwa daga cutuka a duk fadin Najeriya.

Ipaye ya ce, tsarin kula da tsabtar muhalli na daya daga cikin muhimman batutuwa da gwamnatin jihar ke mayar da hankali a kai domin tabbatar da kare lafiyar al'ummarta.

Ya ce, idan aka tsabtace muhalli, musamman tsabtar wajen zama, da ruwan sha, to za'a iya kaucewa kamuwa daga cutar kwalara.

Ya kara da cewa, aikin giggina gadoji da magudanan ruwa da ake gudanarwa a duk fadin jihar na daga cikin matakai da za su tabbatar da tsabtar muhalli.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China