in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar kwalara ta hallaka mutum guda da kwantar da mutane 24 a Tanzania
2017-11-27 09:28:49 cri

Mutum guda ya rasa ransa, kana an kwantar da wasu mutane 24 a asibiti sakamakon barkewar cutar kwalara a gundumar Kyela dake kudu maso yammacin Tanzaniya.

Jami'ar kiwon lafiya ta gundumar Kyela, Mariam Gwere, ta tabbatar da mutuwar, ta ce an samu rahoton bullar cutar na farko ne a ranar 17 ga watan Nuwamba, kuma ba tare da bata lokaci ba aka sanar da jama'a da su hanzarta daukar matakan kare kansu.

Jami'ar ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sun haramta yin gangami da taruwar jama'a a gundumar, ta kara da cewa, barkewar cutar tana da nasaba da rashin tsabta, da shan gurbataccen ruwa da kuma rashin isassun bandakuna a yankunan da lamarin ya faru.

Gwere ta ce, an dauki dukkan matakan dakile bazuwar cutar, kana an tura jami'an kiwon lafiya zuwa yankunan da lamarin ya afku.

Daraktan gundumar Kyela Mussa Mgatta ya bayyana cewa, an kebe wasu yankuna na musamman 3 wadanda za'a yi amfani da su wajen duba wadanda suka kamu da cutar kwalarar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China