in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe: An gudanar da murnar cika shekaru 38 da samun 'yancin kai
2018-04-19 15:05:26 cri

Jiya Laraba 18 ga watan nan ne aka gudanar da bikin murnar cika shekaru 38 da samun 'yancin kan kasar Zimbabwe, an yi taron ne a filin wasan motsa jiki na birnin Harare, fadar mulkin kasar.

Yayin bikin, shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya yi kira ga duk wata jam'iyya wadda ke fatan shiga babban zaben kasar na bana, da ta yi watsi da amfani da karfin tuwa. Ya kuma yi fatan gudanar babban zaben kasar cikin adalci, ta yadda zai samu amincewa daga dukkanin jama'ar kasar.

Wannan biki ya zama irin sa na farko da Zimbabwe ta yi, tun bayan rikicin siyasa da ya auku a watan Nuwambar bara. An kuma yi masa lakabi da "Farfado da tattalin arzikin al'umma, da sake shiga cikin al'ummar duniya".

A cikin jawabin na sa, Mista Emmerson Mnangagwa ya sanar da ci gaban da aka samu, tun bayan da ya hau kan kujerar mulkin kasar a karshen watan Nuwamba na shekarar bara a fuskar tattalin arziki da kyautata rayuwar al'umma. Yayin da ya tabo ziyarar da ya gudanar a kasar Sin a wannan shekara, ya ce wannan ziyara ta zama babban ci gaban da ya samu a fuskar diplomasiyya, tun bayan da ya zama shugaban kasar. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China