in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bakin haure 5 sun nutse kana an ceto wasu 191 a tekun yammacin Libya
2018-06-19 10:11:29 cri
Kimanin bakin haure biyar ne suka hallaka yayin da wasu 191 aka samu nasarar ceto su a tekun yammacin kasar Libya a jiya Litinin, kakakin sojojin ruwan Libya ne ya tabbatar da hakan.

Ayob Qassem yace, dakarun tsaron tekun kasar sun kai samame har sau biyu, inda a samamen farko sun yi tafiyar nisan mil 8 zuwa yankin garin Mellita wanda ke birnin Zuwara, dake da tazarar kilomita 120 a yammacin birnin Tripoli, kana sun ceto bakin hauren 115 a cikin wani kwale kwale na roba.

Bakin hauren dai sun shiga cikin wani mawuyacin hali ne yayin da igiyar ruwa ta illata karamin jirgin ruwan da suke ciki lamarin da ya kekketa jirgin, har ruwa ya samu damar malala cikinsa. Wasu daga cikin bakin hauren sun fada cikin tekun inda nan take suka nitse, inji Qassem.

Kakakin sojojin ruwan yace, an tafi da wadanda aka ceto din zuwa sansanin sojojin ruwa dake Tripoli, inda aka samar musu da kayayyakin jinkai da taimakon magunguna. Daga bisani kuma aka mika su ga sashen dake yaki da bakin haure a Tripoli.

Qassem ya kara da cewa, an ceto wasu bakin hauren 76 daga wasu kasashen Afrika daban daban a wani samamen da suka kai a gabar tekun birnin Zawiya, mai tazarar kilomita 45 daga yammacin Tripoli, suma tuni aka damka su ga hukumar dake yake da bakin hauren.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China