MDD ta fitar da rahoton "Burin neman dauwamammen ci gaba na shekarar 2018" a jiya Laraba, inda ta yi bincike da nazari kan yadda aka aiwatar da shirye-shirye guda 17 wadanda jadawalin neman dauwamammen ci gaba zuwa shekarar 2030 ya shafa. Cikin rahoton, an bayyana cewa, cikin dogon lokacin da ya gabata, an sassauta matsalar karancin abinci, amma, a 'yan shekarun nan, matsalar ta tsananta.
An ce, adadin masu fama da matsanancin karancin abinci ya karu daga mutane miliyan 777 a shekarar 2015 zuwa miliyan 815 a shekarar 2016, kana, adadin da ya kai kashi 10.6 bisa dari na dukkanin al'ummomin duniya a shekarar 2015, yayin da ya kai kashi 11 bisa dari a shekarar 2016. (Maryam)