in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Zaman lafiya zai tabbata ne ta hanyar kaucewa salon shugabanci na son zuciya
2018-06-19 10:28:48 cri
Kwamishinan MDD mai kula da sashen kare hakkin adam Zeid Ra'ad Al Hussein ya bayyana cewa zaman lafiya zai tabbane ne muddin aka gujewa shugabanci na son rai.

Da yake jawabi a taron majalisar kare hakkin 'dan Adam karo na 38 na MDD, wanda aka bude a jiya Litinin a yankin Palais des na birnin Geneva, Zeid ya ce, tsarin shugabanci na kama-karya shi ne babban abin da MDD take adawa da shi, kuma ya kasance abin kyama ga tsarin MDDr.

Ya kara da cewa, wannan shi ne babban taron kasa da kasa na majalisar kare hakkin 'dan Adam da jami'in zai halarta na karshe kasancewar a watan Augusta mai zuwa ne wa'adin aikinsa zai kare, babban jami'in MDDr ya ja hankalin kasa da kasa game da mutunta hakkin 'dan Adam kana ya nuna damuwa game da yawaitar kaddamar da hare hare wadanda suka ci karo da tsarin dokar kare hakkin 'dan Adam.

Haka zalika ya bayyana halin da ake ciki game da batun kare hakkin 'dan Adam a kasashen duniya da dama, ya kara da cewa, kofa a bude take ga dukkan wani yunkurin hada gwiwa da tsarin kare hakkin 'dan Adam na kasa da kasa wanda zai samar da yananin zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al'umma.

Babban taron majalisar kare hakkin 'dan Adam karo na 38 zai gudana ne tsakanin ranakun 18 ga watan Yuni zuwa 6 ga wata Yuli. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China