Zeid ya ce, bisa halin da ake ciki a duniya a yanzu, kamata ya yi Amurka ta kara azama, maimakon ta ja da baya, Zeid ya furta hakan ne biyowa bayan matakin da Amurkar ta dauka na baya bayan nan na janyewa daga kwamitin kare hakkin dan adam na MDDr.
Haka zalika bayan sanarwar da Amurkar ta fitar na janyewarta, shugaban kwamitin kare hakkin dan adam na MDD Vojislav Suc ya nanata cewa, abu mafi muhimmanci shi ne a dauki kwararan matakai kuma kwamitin majalisar ya tsaya tsayin daka a wannan yanayin da ake ciki tare da hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa domin tunkarar kalubalolin da tsarin kare hakkin dan adam ke fuskanta a kullum. (Ahmad Fagam)