in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya bukaci a hada kai, nuna tausayi da daukar matakan tallafawa 'yan gudun hijira
2018-06-20 10:21:15 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bukaci a hada kai, da nuna tausayi da kuma daukar matakai a game da yanayin da 'yan gudun hijira ke ciki a yayin tunawa da zagayowar ranar 'yan gudun hijira ta duniya wanda ta kasance 20 ga watan Yuni

Ya ce a wannan rana ta 'yan gudun hijira ta duniya, dole ne kowa ya yi tunani game da irin abin da za'a yi domin taimaka musu. Amsar wannan ta shafi yin hadin kai ne da yin hadin gwiwa.

A halin da ake ciki a yanzu, akwai sama da mutane miliyan 68 a fadin duniya wadanda ko 'yan gudun hijira ne ko kuma wadanda suka kauracewa matsugunansu a sanadiyyar tashe tashen hankula ko matsin lamba. Wannan adadi ya kai yawan mutanen kasa ta 20 mafi yawan jama'a a duniya.

A shekarar bara, ana iya samun mutum guda dake barin matsuguninsa cikin kowace dakika, mafi yawa daga cikinsu daga kasashe ne da suka fi fama da talauci, in ji babban sakataren MDDr.

Ya ce ya damu matuka bisa yadda ake kara samun yawaitar 'yan gudun hijira wadanda ke cikin matsanancin hali ba su samun irin kariyar da ta dace su samu. Akwai bukatar a sake tsara hanyoyin da za su bada kariya ga 'yan gudun hijirar a matakan kasa da kasa, ya kara da cewa, a halin yanzu a wannan duniyar, babu wata al'umma ko kasa da ta tabbatar da cikakken tsaro ga mutanen da yaki ya daidaita daga matsugunansu ko kuma wadanda aka tilastawa barin gidajensu galibi sun kasance su kadai ne ko kuma ba su samu wani taimako. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China