Cikin wata sanarwar da ya fitar ta hannun kakakinsa Stephane Dujarric, Guterres ya kuma yabawa shugaba Henry Rajaonarimampianina da dukkan masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar game da matsayar da suka cimma na kare muradun al'ummar kasar.
Jami'in na MDD ya kuma yi kira ga masu fada a ji a harkokin siyasar kasar, da su karfafa yin tattaunawa don kare irin ci gaban da aka samu a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya da dorewa mulkin demokiradiya da ma ci gaban kasar baki daya.
Guterres ya kuma nanata kudurin MDD na ganin an gudanar da ingantattun zabukan kasar na wannan shekarar lami lafiya kamar yadda kudin tsarin mulkin kasar ya tanada. (Ibrahim)