in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin kawa ce mai muhimmanci ta Afirka, in ji mataimakin shugaban AU
2016-07-16 13:12:00 cri

Mataimakin shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU Erastus Mwencha ya bayyana jiya Jumma'a a Kigali, babban birnin kasar Ruwanda, cewar kasar Sin kawa ce mai muhimmanci ta nahiyar Afirka wajen hadin gwiwa a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare. Kasashen Afirka sun karu sosai a cikin ayyukan hadin kai tare da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da cinikayya, kiwon lafiya da kuma tsaro.

Mr. Mwencha ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka kira kafin kaddamar da taron koli karo na 27 na kungiyar AU, cewar a cikin 'yan shekarun nan, harkokin cinikayya a tsakanin Sin da Afirka sun samu saurin bunkasuwa, har ma jimillar cinikayya ta zarce dalar Amurka biliyan 200. Haka kuma sakamakon taimakon da Sin ke bayarwa, kasashen Afirka sun samu nasarar yaki da cutar Ebola, suna kuma kokarin gina cibiyoyin rigakafi da shawo kan sauran cututtuka na Afirka. A waje daya kuma, kasar Sin ta nuna himma da kwazo wajen shiga aikin wanzar da zaman lafiya a Afirka, bangarorin biyu kuma sun hada kansu a fannoni shimfida zaman lafiya da tsaro yadda ya kamata.

Bugu da kari, Mr. Mwencha ya ce, Afirka da Sin na aiwatar da sakamakon da aka samu a yayin taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a shekarar bara. Nan gaba kuma, za su mai da hankali kan hadin kansu a fannonin masana'antu, raya muhimman ababen more rayuwa, da rage yawan masu fama da kangin talauci, wadanda aka riga aka kaddamar da wasu daga cikinsu. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China