in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta baiwa Libya kayayyakin agaji na jinya
2018-06-12 10:13:11 cri

A jiya ne, kasar Sin ta baiwa ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Libya kyautan kayayyakin jinya.

Jami'in ofishin jakadancin Sin dake Libya Mista Wang Qimin da ministan kiwon lafiya na kasar Libya Bashir ne suka sa hannu kan takardar mika kayayyakin agajin a birnin Tripoli hedkwatar kasar.

Wang Qimin ya shedawa manema labarai cewa, wadannan kayayyakin agaji sun kunshi magunguna, kayayyakin jinya da dai sauransu. Wannan wani bangare ne na taimakon jinya da Sin take baiwa Libya. Ban da kayayyakin, Sin ta kuma horas da masu aikin jinya na Libya.

A nasa bangare, Bashir ya ce, a shekarun baya-bayan nan Sin ta baiwa kasarsa taimako iri daban-daban a wannan fanni, kuma taimakon kayayyakin agaji da ta ba ta a wannan karo ya kara dankon zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.

Ya kara da cewa, an adana wadannan kayayyaki a dakin ajiyar kayayyakin ma'aikatar kiwon lafiyar kasar, za kuma a raba su ne a yankuna da wurare dake matukar bukata. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China