Lu Kang wanda ya sanar da hakan yayin taron manema labarai a yau Jumma'a, ya ce shugabannin biyu sun kuma tabbatar da matsaya daya game da kawar da nukiliya a yankin. Bugu da kari sun amince su ci gaba da yin tattaunawa wajen ganin an cimma yarjejeniyar zaman lafiya, bayan ganawar farko da shugabannin biyu suka yi a yau Jumma'a a kauyen Panmunjom.
Madam Hua ta kara da dewa, shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa da takwaransa Moon Jae-in na Koriya ta Kudu, sun kuma sanya hannu a kan sanarwar hadin gwiwar, mai taken "sanarwar zaman lafiya da hadewar zirin Koriya ta Panmunjom" wanda ya gudana a gidan zaman lafiya dake yankin Koriya ta kudu, kusa da kauyen da aka sanya hannu kan yarjejeniyar kawo karshen yakin kasashen biyu a shekarar 1953. (Ibrahim Yaya)