Da yake bayyana hakan yayin taron manema labarai a Litinin din nan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Lu Kang ya ce matakin na Koriya ta arewa ya nuna kyakkyawar aniyarta, ta kawo karshen makaman nukiliya a zirin koriya, tare da karfafa amincewa da juna tsakanin kasashe masu ruwa da tsaki a batun nukiliyar kasar.
Jami'in na Sin, ya ce hakan wani mataki ne da ya dace da burin da aka sanya gaba, game da warware batun makaman nukiliya a zirin koriya ta hanyar lumana, wanda kuma ya dace dukkanin sassa su ba shi goyon baya da tallafin da ya kamata. (Saminu Hassan)